Ƴanbindiga sun yi garkuwa da kansiloli biyu da ke wakiltar Gidan Goga da Tsibiri a karamar hukumar Maradun ta jihar Zamfara.
An sace su ne a gaban gidajensu da ke yankin Tsauni misalin ƙarfe 6:50 na yammacin Laraba, bayan sun kammala sallar Magrib suna hutawa.
Unguwar Tsauni a baya ta kasance mafaka ga mutanen ƙauyukan da yan bindiga suka raba da matsuguni sakamakon hare-hare.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar Zamfara, DSP Yazid Abubakar, ya tabbatar da faruwar lamarin kamar yadda gidan talabijin na TVC NEWS ya ruwaito.
Ya ce rundunar ta tura jami’anta zuwa yankin kuma ana ci gaba da ƙoƙari don ceto waɗanda aka sace tare da kama waɗanda suka aikata laifin.
’Yan sanda sun sake jaddada kira ga al’umma da su rika ba da bayanai masu amfani game da ayyuka ko motsin ‘yan ta’adda.
Kawo lokacin haɗa wannan rahoto, ba a samu kiran waya ko wani bayani daga masu garkuwa da mutanen ba.
