
Shugaban Hukumar NACTAL na kasa Abdulganiyu Abubakar tare da rakiyar wasu Shuwagabannin yanki da kuma na Ofishin Hukumar ta NACTAL matakin Kasa sun kai ziyara ga Kwanturola Janar ta Hukumar Shige da Fice ta kasa Kemi Nanna domin tattauna Muhimman Batutuwa da kuma Neman Hadin kan Juna.
Shugaban Kungiyar ta NACTAL ya Godewa Shugabar Hukumar ta Shige da Fice na basu damar ganawa da juna duk da tarin Ayukka da suke Gabanta.
Hakama ya taya ta murna akan tsawaita Kwantiragin ta da Shugaban kasa Bola Tinubu yayi, yayin da yake tuna irin Kyakkyawar alakar Aiki da ke tsakanin Hukumomin biyu da irin yadda Hukumar ta ke basu goyon baya da Hadin kai Musamman a bangaren da ya shafi safarar Biladama.
Ya kuma kara da jinjinawa Shugabar Hukumar akan yadda take bada Fifiko a bangaren Bunkasa jin dadi da walwalar jami’an ta wanda yace hakan ya kara zaburar dasu domin kara dukufa akan ayukkan su.
Shugaban na NACTAL ya kuma kara zayyano wasu karin cigaba da aka samu a Lokacin Shugabancin ta da suka hada da bayarda kariya ga ma’aikatan NACTAL a lokutan Aiki daban-daban.
A nata Bangaren Shugabar Hukumar ta Shige da Fice Kemi Nanna tace godewa NACTAL akan Ziyarar wanda tace tazo a lokacin da ya kamata.
“Munada Kyakkyawar kuma dadaddiyar alakar aiki wanda zan tabbatar da inganta ta inji Kemi Nanna.
Ta godewa Shugaban na NACTAL akan yunkurin sa na ci gaba da aiki tare, wanda tace hakan zai kara musu kwarin Gwuiwa Musamman a kan ayukkan su na iyakokin Kasa.