
Ambaliya ta mamaye gidaje da dama da kuma kasuwanci a Lagos Island da wasu sassan jihar sakamakon ruwan sama da ka sheƙa kama da bakin kwarya a ranar Talata.
Ruwan sun mamaye Mile 2, Lekki Phase 1, Lekki Expressway, 3rd Mainland Bridge, Ago Palace Way, Ayobo-Ipaja, Fola Osibo da kuma Sangotedo.
A cikin wani rubutu a X ranar Laraba, mazauna yankin sun ɗora laifin matsalar kan toshewar magudanar ruwa, lamarin da ya tilasta matafiya barin motoci su rika yin tafiya mai nisa da ƙafa.
Bidiyon ya nuna motocin haya da babura na famar wucewa a kan titunan da suka cika da ruwa kamar yadda jaridar TheCable ta ruwaito.
Wani mai amfani da X, @JustOzed, ya wallafa cewa: “Tun da safe yau, 23 ga Satumba, wasu sassan Lagos ciki har da Ago Palace Way (Apple Junction, Ago Bridge) da Mile 2, ruwa ya mamaye su. Na ɗauki wannan faifan bidiyo domin nuna gaskiyar da muke fuskanta a kowanne lokacin damina.”
A cikin wata sanarwa a ranar Laraba, kwamishinan muhalli da albarkatun ruwa na jihar Lagos, Tokunbo Wahab, ya jajanta wa al’ummar da ambaliyar ta shafa.
Wahab ya bayyana cewa Lagos, kasancewarta birni da ke bakin teku, tana da saukin samun ambaliyar ruwa musamman idan aka samu ruwan sama mai yawa.
Ya ce gwamnatin jihar na ci gaba da tsaftacewa da kuma aiwatar da dokokin muhalli don rage matsalar ambaliya.
