
A jiya, ƙwararan hujjoji sun ƙara bayyana cewa tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso yana tattaunawa da shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentwe Yelwtda a kan shirinsa na komawa jam’iyyar.
Majiyoyi daga jam’iyyar APC ta jihar Kano, sun ce Kwankwaso ya rubuta wa sakatariyar jam’iyar APC ta ƙasa da ke Abuja, inda ya sanar da jam’iyyar shirinsa na komawa a cikin ta kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Sai dai jaridar Daily Trust ba ta tantance gaskiyar wannan labari ba kawo lokacin haɗa wannan rahoton.
Haka kuma, wata majiya daga sakatariyar jam’iyar APC ta ƙasa da ke Abuja, ta ce Kwankwaso da shugaban jam’iyyar na ƙasa na gudanar da wata tattaunawa domin komawar Kwankwaso a jam’iyyar kuma tattaunawar ta yi nisa.
