
Da yake ƙaddamar da kayyakin a hukumar samarwa da adana magunguna ta jihar Sakkwato, manajan shirin Aspire Project na kungiyar Plan International, Malam Murtala Bello, ya ce wannan na daga cikin shirinsu na Aspire da suke aiwatarwa a jihohin Bauchi da Sakkwato.
Malam Bello ya ce bayan sun gudanar da bincike a makarantu sama da 100 a Sakkwato a shekarar da ta gabata, sun samu nasarar gyara ajujuwa a wasu makarantu guda biyar ciki har da makarantar sakandaren je-ka-ka-dawo ta gwamnati da ke Moreh da kuma makarantar A A Raji da dai sauransu.
A jawabinsa, kwamishinan lamurran addini na jiha, Dr Jabir Sani Maihula wanda ya samu wakilcin babban sakataren ma’aikatar, Dr Sani Labaran ya ce ƙungiyar Plan International ta daɗe tana taimaka wa gwamnatin jihar Sakkwato ta fannin ilimi da lafiya.
Ya kuma nanata cewa kayayyakin waɗanda suka shafi na tsaftar jiki da ta muhalli suna da inganci sosai, inda ya bukaci waɗanda za su amfana da su yi amfani da su yadda dace.
Shi ma da yake jawabi daraktan bukumar samarwa da adana magunguna ta jihar Sakkwato, Ghazali Attahiru Gwadabawa, ya yaba wa ƙungiyar Plan International bisa kokarinta tallafa wa gwamnatin jiha.
Daga cikin kayan da aka raɓa sun haɗa da: tabarmi, butocin sallah, allunan rubutu da maka da tsintsiya da robobin zuba ruwa da na zuba shara da dai sauran kayayyaki.
