
Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yi kira ga Bankin Duniya da Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF), da Bankin Raya Afirka (AfDB) da su ƙara yawan kuɗaɗen da suke warewa domin yaƙi da matsalar sauyin yanayi.
Tinubu, wanda mataimakinsa Sanata Kashim Shettima ya wakilta, ya yi wannan kira ne a taron sauyin yanayi yayin zaman babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80 a birnin New York na Amurka.
Shugaban ya bayyana cewa matsalar sauyin yanayi tana buƙatar aiki ba wai magana da fatar baki kaɗai ba, inda ya ce an haɗa da jajircewa da maida himma.
Tinubu ya ce Najeriya na shirin tara dala biliyan 20 zuwa 25 na kuɗaɗen sauyin yanayi nan da shekarar 2030, domin yaƙi da wannan matsalar, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Ya kuma yi kira ga kungiyoyin ƙasa da ƙasa abokan ƙawance da su ƙara tallafin kuɗaɗe suke wayewa da musayar ilimi da fasahar zamani domin gaggauta kawo ƙarshen matsalar ba a Najeriya kaɗai ba, har ma da Afirka baki ɗaya wajen samar da kyakkyawan yanayi.
