Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya bar birnin New York, Amurka, zuwa Jamus bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaman taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80.
A lokacin taron, Shettima ya samu yabo daga Sakataren Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, António Guterres, kan yunƙurin Najeriya na neman samun kujerar dindindin a Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya.
Haka kuma ya gabatar da damar da Najeriya take da ita ta sauyin makamashi mai darajar dala biliyan $200 ga masu zuba jari na duniya, tare da ƙarfafa haɗin gwiwar dabarun kasuwanci, tsaro da batun ƙaurar jama’a ga Birtaniya.
Shettima ya kuma gabatar da jawabin Shugaba Tinubu a lokacin taron, inda ya yi kira ga sake fasalin Majalisar Ɗinkin Duniya da neman kujerar dindindin ga Najeriya a Kwamitin Tsaro na MDD, tare da buƙatar a bar Afirka ta riƙe ikon mallakar dukiyar ma’adananta da ta kai darajar dala biliyan $700, da kuma shirin haɗa Afirka da fasahar sadarwa ta zamani.
Bugu da ƙari, ya gana da Gidauniyar Gates kan batutuwan kiwon lafiya da ilimi, inda ya bayyana Najeriya a matsayin cibiyar cinikayyar Afirka (AfCFTA) mai darajar dala tiriliyan $3.4.
