
Tsohon babban Hafsan Sojin Najeriya, Janar Lucky Irabor, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta ƙaddamar da yaƙi a kan ƴan bindiga da ƴan ta’adda da ke addabar Najeriya.
A cewarsa, babu wasu takardun doka da ke nuna cewa Najeriya tana cikin yaƙi.
“Babu wasu takardu na doka da ke nuna cewa Najeriya tana cikin yaƙi. Babu; muna tunanin kawai muna cikin yaƙi.” cewar lrabor.
Ya ƙara da cewa, “Tabbas, akwai buƙatar ayyana yaƙi domin tattara dukkanin ƙarfin gwamnati kai tsaye zuwa zuwa yaƙi ,” in ji janar a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels, a ranar Litinin.
Irabor ya bayyana cewa idan an ayyana yaƙi, za a tura kayayyakin aiki kai tsaye domin fatattakar masu aikata laifukan.
