
Ministan Ƙirƙira, Kimiyya da Fasaha, Uche Nnaji, ya yi murabus daga gwamnatin Shugabar Bola Ahmed Tinubu.
Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ne ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa a ranar Talata.
Wannan kuwa biyo bayan zargin da ake yi masa da gabatar da takardan shedar digiri ta jabu kamar yadda jaridar Premium Times ta bankaɗo a cikin wani bincike da ta gudanar.
