
A jihar ta Sakkwaton dake daya daga cikin Jihohin Arewacin kasar nan na fama da Matsalar Ruwan sha.
Wannan Matsalar ta ruwa na daya daga cikin Matsalolin da ke ciwa Al’ummar Jihar tuwo a kwarya duk kuwa da matakan da Hukumomin jihar ke cewa suna dauka.
A kullum rana ta Allah sai an hango mata matasa na Kokarin samun ruwan da zasuyi amfanin yau da kullum.
A zantawar da Jikan Babi Radio sukayi da wasu Al’ummar Jihar ta Sakkwato sun bayyana irin damuwa da tashin hankali da suke ciki sanadiyyar rashin samun ruwan, wanda suka ce yana dagula musu lissafin komai na rayuwa.
Sun bayyana cewa, ruwan wanki ko wanka ma wahala suke musu, kai hatta da ruwan da zasu sha wani lokaci suna musu tarnaki.
Gwamnatin Jihar ta Sakkwato dai tace tana kokarin ganin ta shawo kan Matsala saidai har yanzu shiru babu amo babu labari.