Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya ASUU ta dakatar da yajin aikin gargadi na makonni biyu da ta shiga
Shugaban kungiyar na ƙasa, Farfesa Chris Piwuna, ne ya bayyana haka yayin taron manema labarai da aka gudanar a Abuja a ranar Laraba.
Ya ce dakatarwar za ta fara aiki ne daga tsakar daren Laraba, 22 ga Oktoba, 2025.
Sai dai Piwuna ya gargadi gwamnati cewa ƙungiyar ba za ta yi wata-wata ba wajen dawo da yajin aikin ba, idan har gwamnati ta kasa biya masu buƙatunsu cikin makonni huɗu masu zuwa.

