
A hukumance, ƙasar Birtaniya ta amince da Falasɗinu a matsayin ƙasa cikakken iko.
Firayim Ministan ƙasar, Sir Keir Starmer, ne ya sanar da hakan a cikin wani saƙo da ya wallafa a shafin X, a ranar Lahadi.
“A yau, domin farfaɗo da fatan samun zaman lafiya tsakanin ’yan Falasɗinu da Isra’ila, da kuma tabbatar da tsarin ƙasashe biyu, Birtaniya ta amince da Falasɗinu a matsayin ƙasa mai cikakken iko,” in ji Firayim Ministan a shafin X.
