
Shugaban kasa Bola Tinubu ya gayyaci tsohon tsohon kantoman riƙon ƙwarya na Jihar Rivers, Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya), zuwa fadar shugaban kasa, Aso Rock Villa da ke Abuja.
Ibas, wanda ya isa fadar shugaban kasa da misalin ƙarfe 5:50 na yamma cikin kayan masu launin ruwan kasa, ya samu rakiyar Ministan Kudi da tattalin arzikin kasa, Wale Edun, da shugaban Hukumar yaƙi da Rashawa ta EFCC, Ola Olukayede.
Tun da farko, Edun ya shiga fadar shugaban kasa amma ya fita da sauri, kafin ya dawo da wani fayil a hannunsa, abin da ya nuna muhimmancin taron.
Ibas ya yi watanni shida a matsayin mai rikon ƙwarya na kujerar gwamnan jihar mai arzikin mai. Ya bar ofis ne a ranar 17 ga Satumba, bayan karewar dokar ta-baci da ta dauki watanni shida, bayan da shugaban kasa ya bada umarnin a dawo da gwamnan jihar da aka dakatar, Sir Siminilayi Fubara da mataimakinsa da kuma ‘yan majalisar dokokin jihar tun daga ranar Alhamis da ta gabata.
Majalisar dokokin Jihar Rivers, karkashin jagorancin Kakakin majalisar, Martin Amaewhule, a zaman ta na farko bayan karewar dokar ta-baci, ta bayyana cewa za ta gudanar da bincike kan yadda aka kashe kudaden jihar a lokacin dokar ta-bacin.
A cewar ƴan majalisar: “Za mu duba yadda aka kashe kuɗaɗe daga babban asusun gwamnati, musamman kan bayar da kwangila da sauran ayyuka a lokacin dokar ta-bacin.”
Sai dai Ibas ya ƙi amincewa da wannan shawarar ta binciken yadda aka kashe kudaden a lokacin mulkinsa.
An ba da rahoton cewa jihar Rivers ta samu aƙalla biliyan N254.37 daga rabon kuɗin FAAC da aka raba tsakanin watan Maris zuwa Agusta 2025, a lokacin da tsohon kantoman ke mulki.
