
Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya sallami dukkan kwamishinoni da jami’an gwamnati da ke aiki a karkashin gwamnatinsa.
Fubara ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaransa, Nelson Chukwudi, ya fitar a birnin Port Harcourt da yammacin Laraba, inda ya ce sallamar ta fara aiki nan take.
Gwamnan ya ce wannan mataki ya biyo bayan hukuncin kotun koli na baya-bayan nan.
Fubara ya kuma gode wa mambobin majalisar zartarwarsa bisa ayyuka gudunmawar da suka bayar wajen ci gaban jihar a cikin shekaru biyu da suka gabata.
Ya yi wannan godiya ne yayin zaman ban kwana da ya gudanar tare da majalisar zartarwarsa domin bikin cika shekaru 65 da samun ’yancin kai Najeriya a fadar gwamnati da ke Port Harcourt, a ranar Laraba.
Sanarwar ta ce, “Gwamnan Jihar Rivers, Sir Siminalayi Fubara, ya gode wa mambobin majalisar zartarwarsa bisa hidima da gudummawar da suka bayar wajen ci gaban jihar a cikin shekaru biyu da suka gabata.”
