
Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya sauke Hajiya Zainab Baban-Takko, kwamishiniyar harkokin mata da ci gaban ƙananan yaradaga mukaminta nan take.
Mai ba wa gwamnan shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Malam Mukhtar Gidado, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka fitar da safiyar wany Litinin.
A cewarsa, wannan mataki ya biyo bayan wasu ƴan sauye-sauye da gwamnan zai yi a Majalisar Zartarwa ta Jihar.
“Saboda haka, an sauke kwamishiniyar harkokin mata da ci gaban ƙananan yara, Hajiya Zainab Baban-Takko, daga mukaminta nan take,” in ji sanarwar.
