
Gwamnan Jihar Enugu, Peter Mbah, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP zuwa APC.
Ya bayyana haka ne a cikin jawabin da ya yi wa al’ummar jihar baki ɗaya a wani taro na musamman.
Gwamnan ya kuma kare matakinsa na sauya sheka, yana mai cewa wannan mataki ya zama dole ne domin haɗa jihar dake Kudu maso gabas da gwamnatin tarayya.
Gwamnan ya bayyana cewa dalilin da ya sa ya sauya sheka shi ne don ƙarfafa haɗin kai da gwamnatin tarayya da kuma kawo ci gaba ga jiharsa.
“Akwai wani lokaci da mutum dole ne ya yanke shawara mai ƙarfi domin tsara makomarsa. A yau, bayan dogon tunani, mun yanke shawarar barin jam’iyyar PDP, mu koma All Progressives Congress,” in ji Mbah.
Ya gode wa jam’iyyar PDP bisa goyon bayan da ta ba shi a tsawon shekaru, yana mai cewa wannan canji yana da muhimmanci domin cimma manufofin gwamnatinsa.
A cewar Mbah, dalilinsa na shiga APC shi ne domin ya yi wa jama’ar Enugu aiki yadda ya kamata, tare da daidaita da hangen nesa na jam’iyyar wajen kawo cigaba da ci gaban ƙasa.
Gwamnan ya sake jaddada aniyarsa ta ci gaba da kare muradun jiharsa, tare da nuna kwarin gwiwa cewa jam’iyyar APC za ta ba shi damar haɗin kai da bunƙasa tattalin arziki.
Ya kuma yaba wa manufofin Shugaba Bola Tinubu, yana mai cewa Jihar Enugu ta amfana sosai da goyon bayan gwamnatin shugaban ƙasa.
Gwamnan na PDP ya koma jam’iyyar mai mulki tare da mambobin majalisar dokoki, kansiloli, shugabannin ƙananan hukumomi da wasu jami’ai.
Rahotanni sun nuna cewa bayan ficewarsa, Gwamnan Jihar Bayelsa, Duoye Diri, ma zai biyo baya, domin shirye-shiryen sauyawarsa zuwa APC sun kusa kammala.
Tun farkon shekarar nan, Gwamnan Jihar Delta, Sheriff Oborevwori, da na Akwa Ibom, Umo Eno, su ma sun sauya sheka zuwa jam’iyyar mai mulki tare da dukan jami’ansu, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.
