
Gwamnatin jihar Sokoto ta umarci dukanin shugabannin makarantun sakandare a jihar da su dakatar da karɓa kuɗaɗe a hannun dalibai.
Kwamishinan ilimin furamare da sakandare na jihar, Prof. Ahmad Ladan Alah, ya jaddada cewa babu dalilin da zai sa a bukaci dalibai, iyaye ko kuma maga’isan yara su biya duk wasu kuɗi.
A cikin wani bayani da jami’in hulɗa da jama’a na ma’aikatar, Ibrahim Muhammad Iya ya fitar, amadadin kwamishinan, ya ce an shawarci dukanin shugabannin makarantun sakandare da su yi ɗa’a ga wannan umarnin.
Sanarwar ta kara da cewa karya wannan dokar zai sa a dauki mataki a kan mutum.
Bayanin ya ce umarnin ya biyo bayan kafa kwamiti da kwamishinan ya yi domin magance damuwar da aka nuna kan kuɗin da ake karɓa à makarantu.
Ya kara da cewa dakatarwar za ta ci gaba da aiki har sai lokacim da kwamitin ya gama bincike tare da gabarar da rahotonsa.
Kudin sun hadar da na PTA da na ba da gurbin karatu da na karɓar sakamakon jarabawa da na MSS da kuma na ga WAEC da NECO da kuma NABTEB.
