
Gwamnatin Sakkwato da UNICEF Za Su Kaddamar da Riga-kafin Shan-inna da Gaida
Gwamnatin Jihar Sokoto haɗin gwiwa da sauran ƙungiyoyi abokan ƙawance za su kaddamar riga-kafin cututukan baƙon-dauro da aka fi sani da suna Gaida nau’in Rubella da shan inna, domin ƙara inganta lafiya tare da kare rayuwar ƙananan yara a fadin jihar.
An sanar da hakan ne a lokacin wani taron Manema Labarai da aka shirya domin sanar da ranar kaddamarwar a ranar Juma’a, 3 ga Oktoba, 2025 a cibiyar kula da masu bukatar kulawar gaggawa da ke Asibitin Kwararru dake Sokoto, inda aka bukace su da su mayar da hankali wajen faɗakarwa da wayar da kan al’umma ta hanyar yada labarai, da gabatar da shirye-shirye a gidajen rediyo da kuma ta kafafen sada zumunta.
A wajen taron, Sabi’u Shehu Gandi, jami’i daga hukumar bunƙasa kiwon lafiya a matakin farko ta jihar Sakkwato, ya jaddada muhimmancin rawar da ‘yan jarida da sauran masu amfani da Kafaffen sada zumunta na zamani wajen isar da saƙonni, ƙaryata jita-jita da kuma ƙarfafa gwiwar iyaye su kai ‘ya’yansu don yin riga-kafi.
Sun ce hadin gwiwar zai taimaka wajen yi wa dukkan yara a fadin Sokoto riga-kafi, ba tare da an bar kowa a baya ba.
Shirin riga-kafin na samun goyon bayan manyan masu ruwa da tsaki kan sha’anin kiwon lafiya da kula da ƙananan yara na Kasa da Kasa irinsu: UNICEF da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), da Kungiyar Tarayyar Turai (EU) da Gavi, da shirin kawar da cutar shan inna.
Kungiyoyin sun kuma yi kira ga iyaye, da shugabannin al’umma da su tabbatar da kai ‘ya’yansu don yin allurar rigakafi, domin a cewar su, riga-kafi na daga cikin hanyoyin da suka fi dacewa wajen kare ƙananan yara daga kamuwa daga cutuka masu kisa.
A lokacin yekuwar da za a gudanar a dukkanin ƙananan hukumomin jihar Sokoto 23 cikin makonni masu zuwa, za a tura jami’an lafiya zuwa gidaje, makarantu da cibiyoyin lafiya domin tabbatar da cewa an bai wa dukkanin yaran da suka cancanta riga-kafin.
