
Gwamnatin Jihar Sokoto ta raba Naira miliyan 293 da kuma buhunan abinci 2,540 ga waɗanda hare-haren ‘yan bindiga suka shafa da kuma ‘yan gudun hijira a ƙananan hukumomin Isa da Sabon Birni.
Gwamna Ahmed Aliyu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labaransa, Abubakar Bawa, ya fitar ranar Juma’a a lokacin da gwamnan ya kai ziyarar jaje ga al’ummomin da abin ya shafa.
A wajen taron, ya bayar da kuɗi da kayan abinci ga iyalan waɗanda aka kashe, wadanda suka ji rauni da kuma ƴan gudun hijira.
A Karamar Hukumar Isa, gwamnan ya bai wa iyalan mutane 65 da aka kashe Naira miliyan biyu kowanne da buhunan shinkafa guda biyar.
Haka kuma, ya bai wa mutane biyar da suka ji rauni Naira dubu 250 kowanne da buhunan shinkafa uku.
Bugu da ƙari, ya ba da tallafin Naira miliyan 20 da buhunan abinci 1,200 ga ƴan gudun hijira, wanda jimlar tallafin a Isa ya kai Naira miliyan 151.25 da buhunan abinci 1,240.
Haka kuma a Sabon Birni, iyalan mutane 61 da aka kashe sun samu Naira miliyan biyu kowanne da buhunan shinkafa biyar.
Gwamnati ta kuma bai wa ƴan gudun hijira Naira miliyan 20 da buhunan abinci 1,200, wanda jimlar tallafin ya kai Naira miliyan 122 da buhunan abinci 1,300.
Gwamna Aliyu ya yi Allah-wadai da ƙaruwar matsalar tsaro a yankin, inda ya gargadi masu bai wa ‘yan bindiga bayanai da cewa gwamnatinsa za ta ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki domin hukunta su.
