
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa, darasin lissafi wajibi ne ga duk ɗaliban da ke rubuta jarabawar kammala babbar Sakandare ta SSCE.
Wannan bayani na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Boriowo Folashade, ta fitar a ranar Lahadi.
A ranar Talata da ta gabata, Boriowo ta sanar da cewa ɗaliban manyan makarantu sakandare na bangaren da ba na kimiyya ba, ba su buƙatar sai sun samu “credit” a Lissafi kafin a ba su gurbin karatu a jami’a ko sauran manyan makarantu.
