
Kungiyar Save the Child Initiative ta bullo da shirin Horar da Malaman Makarantu da suke a yankunan Sakkwato ta Arewa da Bodinga da kuma Tambuwal.
Wannan Taron Horarwar na kwanaki hudu ya gayyato Shuwagabannin Kungiyoyin ilimi da Malaman Makarantun Sakandare a Kananan Hukumomin.
Wannan taron yana da Manufar Tallafawa dalibai da kuma Basu horo lokaci bayan lokaci domin tabbatar da Karatu mai Inganci ga Daliban Furamare da kuma Karamar Sakandare.
Hakama a lokacin taron za,a lalubo hanyoyin magance Matsalolin da malaman ke Fuskanta, da kuma basu horo da Karafa musu Gwuiwa akan ayukkan su.
Wannan taron bayan kammala shi ana sa ran Mahalartan sa zasu koma yankunan su domin horar da malaman Sakandaren da aka zakulo daga Kananan Hukumomin guda uku.
Idan aka baiwa malaman Horo ana sa ran Kimanin Fiye da Yara Miliyan 1 da dubu 300 zasu amfana kai tsaye.