Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyar NNPP a babban zaben 2023, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ƙarya rahotanni da ke yawo a kafafen sada zumunta na zamani cewa ya rubuta wa sakatariyar APC ta ƙasa domin sanar da ita shirinsa na komawa jam’iyyar.
Kwankwaso, a cikin wani bayani da ya wallafa a shafinsa na Facebook, a wannan Jumu’a, 26 ga watan Satumbar 2025, ya ce babu wata wasiƙa da suka miƙa wa wata jam’iyyar siyasa.
“Muna so ku sani cewa babu wata takarda da muka gabatar ga duk wata jam’iyya,” in ji Kwankwaso a cikin sanarwar da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
A don haka, ya shawarci jama’a da su kasance a faɗake domin samun sahihan bayanai ta hanyar da ta dace.
Tun da farko jaridar Daily Trust ta ba da rahoton cewa Kwankwaso ya gabatar da wasiƙa ga sakatariyar jam’iyar APC ta ƙasa, inda yake sanar da ita kan shirinsa komawa a cikin jam’iyyar.
Rahoton ya kuma ƙara da cewa wasu majiyoyi sunce tattaunawa ta yi nisa tsakanin Kwankwaso da kuma shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Nentawe Yelwtda.
