
Majalissar magabata ta ƙasa ta aminta da naɗin Farfesa Joash Ojo Amopitan, SAN a matsayin sabon shugaban hukumar zaɓe ta ƙasa INEC.
Wani bayani da hadimin shugaban kasa Bola Tinibu kan sha’anin yaɗa labaraia, Bayo Onanuga ya wallafa a shafin X, ya ce shugaba Tinibu ya gabatatar da sunan Amopitan ga majalissar ne a lokacin taronta a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Shugaba Tinibu ya faɗa wa majalissar cewa, Amopitan mai shekaru 58, shehin malami a fannin Shari’a daga jihar Kogi, shi ne mutum na farko daga jihar Arewa ta tsakiya da aka miƙa sunansa domin naɗa shi a muƙamin.
Bayanin ya ce naɗin ya biyo bayan saukar Prof. Mahmood Yakubu wanda wa’adinsa ya ƙare bayan kammala shekara 10 a watan Okotoban nan da muke ciki.
