
Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yi afuwa ga mutane 175 da aka yanke wa hukunci kan laifuka daban-daban, ciki har da Maryam Sanda, wadda aka yanke wa hukuncin kisa bayan ta kashe mijinta a shekarar 2017.
Wannan afuwa, wadda aka bayar bisa ikon shugaban ƙasa, ta shafi manyan mutane, fursunonin siyasa, da kuma waɗanda suka daɗe a gidajen gyaran hali daban-daban.
Mai taimaka wa shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Asabar, inda ya ce jerin sunayen sun haɗa da masu haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba da masu laifin ofis da masu laifin miyagun ƙwayoyi da suka nuna nadama, da kuma wasu baƙin haure.
