
Kungiyar The Future is Now ta nemi a bai wa matasa kashi 70% na Kujerun Majalisar Wakilai da majalisun dokoki na jihohi a fadin Najeriya.
Sun gabatar da wannan buƙata ne a wajen ƙaddamar da ƙungiyar a Otal ɗin Nicon Luxury da ke Abuja, a ranar Laraba.
Shugabannin matasa da masu ruwa da tsaki daga sassan Najeriya ne suka halarci taron.
Mahalarta taron sun amince cewa lokaci ya yi da matasa za su nemi gurabu domin su riƙa ba da tasu gudunmawa wajen ba da shawarwari da kuma fito da tsare-tsare.
Sun jaddada cewa matasan Najeriya ba shugabannin gobeba ne kawai, shugabanni ne har ma a yau.
Da yake jawabi a wajen taron, wanda ya shirya taron, tsohon mai taimaka wa shugaban ƙasa, Laolu Akande, ya ce shirin na nazarin ɗaukar ƙwararan matakai kafin zaɓe mai zuwa.
