
Matatar mai ta Dangote ta ci gaba da sayar da man fetur da kuɗin Naira cikin ƙasa da sa’o’i 24 bayan dakatar da sayarwar.
Wannan sauyin ya biyo bayan shiga tsakanin da Shugaban Kwamitin sayar da Man Fetur da kuɗin Naira, Dr Zacch Adedeji, ya yi wanda kuma shi ne Shugaban Hukumar Tara Haraji ta Ƙasa (FIRS).
Matakin ya fuskanci ƙalubale sakamakon ƙarancin isasshen ɗanyen man da ake samu.
A ranar Juma’a, matatar mai ta Dangote ta sanar da abokan cinikinta cewa daga ranar Lahadi, 28 ga Satumba, 2025, za ta dakatar da sayar da kuɗin Naira.
Sai dai, cikin ƙasa da sa’o’i 24, kamfanin ya fitar da sanarwa ga abokan ciniki yana bayyana cewa za a ci gaba da sayar da man a Naira, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Sanarwar ta ce: “Biyo bayan shiga tsakani na Shugaban Kwamitin sayar da mai da kuɗin Naira, muna farin cikin sanar da ku cewa an ci gaba da sayar a Naira ba tare da ɓata lokaci ba
