
Gwamnan Jihar Sokoto, Ahmad Aliyu, ya jaddada kudirin gwamnatinsa na magance matsalar tsaro musamman ta ƴan bindiga, wadda ta daɗe tana addabar jihar da sauran sassan Arewa maso Yammacin Nigeria.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Sokoto kamar sauran jihohin Arewa maso Yamma, na ci gaba da fama da hare-haren ‘yan bindiga da kashe-kashe.
Da yake jawabi a Abuja ranar Talata bayan karɓar lambar yabo ta karramawa daga ƙungiyar Nigeria First Integrity Group tare da haɗin gwiwar All Progressives Stakeholders, Aliyu ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta kuduri aniyar samar da tsaro da kuma inganta walwalar jama’a.
Ya ce: “Babu wani ɓangare da gwamnatin Sokoto za ta bari a ƙoƙarin magance matsalar tsaro a faɗin jihar. Za mu ci gaba da ɗaukar dukkanin matakan da suka dace domin samar da tsaro ga al’ummarmu da kuma inganta rayukansu”.
Gwamnan, wanda kwamishinan ƙananan Hukumomi, Ibraheem Adare, ya wakilta, ya bayyana tsaro da ilimi a matsayin ɗaya daga cikin manyan ƙudurorin gwamnatinsa guda tara.
