Rundunar ‘yansanda a Abuja babban birnin Najeriya ta ce ta yi nasarar kashe ‘yanbindiga uku bayan kuɓutar da mutanen da suke garkuwa da su.
Cikin wata sanarwa, kakakin rundunar Josephine Adeh ta ce kafin kashe su gungun ‘yanbinidigar sun yi yunƙurin sace wasu ‘yanmata biyu a yankin Guzape, amma ɗaukin da dakarun rundunar suka kai ya sa ska kuɓutar da su. Sai dai wani ɗan sa-kai Bako Pwaza ya rasa ran sa a yunƙurin.
“A ranar Laraba ma, gungun suka sace wani mai suna Nafiu Idris a Karu. Bayan tattara bayanan sirri dakaru suka kai samame maɓoyarsu a Dajin Zinda mai maƙwabtaka da jihara Nasarawa bisa rakiyar mafarauta,” in ji ta
