
Shirin nan dake tallafawa Ilimin yaya mata a Makarantu Agile Hadin Gwuiwa da Kungiyar Save the Child Initiative sun kaddamar da wani Shirin Horar da Malaman Makarantu domin koyawa Yan mata yadda zasu tsaftace jiki da kuma koya masu sana’oin hannu.
Wannnan Shirin wanda aka kaddamar a Jihar Sakkwato ya zakulo Makarantun sakandare Fiye da 100 da suke cikin Kwaryar Birni da sauran Kananan Hukumomi.
Shirin dai nada Manufar kara Kimtsa Yara mata domin su iya bayyana Damuwar su ga Malaman nasu da kuma koya musu yadda zasu tsafatce jikin su Musamman lokacin Al’ada.
Mairo Rabi’u Sharif daga Shirin na Agile tace ko bayaga tsafta da za’a koyawa matan yan sakandare, akwai kuma Bangaren sana’oi wanda zai bada damar Koya musu Dinkin Tela, Koyon Man shampoo, da sauran sana’oin hannu.
Mairo Sharif tace idan suka kammala karatu da sana’oi zasu taimakawa mazajen su wajen rage dawainiyar cikin Gida.
Rabi’u Gandi na Kungiyar Save the Child Initiative yace idan Har iyaye suka basu dama to ko shakka babu wannan Shirin zai zama mai Alfanu ga matan da su kansu iyayen.
Rabi’u Gandi yace, wannan soman tabi ne domin akwai ire-iren wadannan Shirye -Shiryen da suke da zimmar tallafawa yara mata a fadin Jihar Sakkwato.
An gudanar da Wannan Horon Bitar ga Malamai Mata da suke fito daga Makarantun sakandaren a Makarantar Sultan Maccido Institute, da GGC Mabera da sauran Makarantu da suke cikin wasu Kananan Hukumomi a Jihar Sakkwato.