
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya koma Abuja bayan kammala ziyarar aiki ta kwanaki goma a Legas.
Shugaban ya isa Legas ranar Juma’a, 26 ga Satumba, bayan halartar naɗin sarautar Olubadan na ƙasar Ibada, Oba Rashidi Ladoja, a Ibadan.
Yayin zamansa a Legas, Shugaba Tinubu ya yi tattaunawa da manyan masu zuba jari, ciki har da Bayo Ogunlesi, Shugaban Kamfanin Global Infrastructure Partners, da Hakeem Bello-Osagie, tsohon Shugaban bankin UBA da Etisalat, yanzu kuma Shugaban kamfanin Metis Capital Partners.
Shugaba Tinubu ya kuma karɓi baƙincin Sakatare-Janar na Hukumar Kula da Harkokin Jiragen Ruwa ta Duniya (IMO), Mista Arsenio Dominguez, tare da Ministan Harkokin Ruwa da Tattalin Arzikin Teku, Adegboyega Oyetola, da wasu shugabannin hukumomi a fannin.
A yayin ganawar, Shugaba Tinubu ya sake tabbatar da kudurin gwamnatinsa na inganta hukumar jiragen ruwa ta Najeriya a matsayin mafita ga harkar makamashi.
A lokacin da Najeriya ke cika shekaru 65 na samun ‘yanci, Shugaba Tinubu ya ziyarci Jihar Imo domin kaddamar da wasu ayyuka da Gwamna Hope Uzodimma ya aiwatar.
Shugaban ya kuma ƙaddamar da littafin da gwamnan ya rubuta, wanda ya bayar da tarihin shekaru 10 na mulkin APC a Najeriya.
Ya kuma gabatar da jawabin a gidan talabijin na kasa daga Fadar Shugaban Kasa ta Dodan Barracks, a ranar bukin ƴancin kai, sannan daga baya ya ƙaddamar da sabuwar cibiyar fasahs ta ƙasa wadda aka gyara aka kuma sauya mata suna zuwa cibiyar fasaha da al’adu ta Wole Soyinka, inda ya yi kira ga ƴan Najeriya su riƙa faɗin alheri game da ƙasarsu.
A ranar Asabar, 4 ga Oktoba, Shugaba Tinubu ya ziyarci birnin Jos na Jihar Plateau, domin halartar jana’izar Mama Lydia Yilwatda, mahaifiyar Farfesa Nantawe Yilwatda, shugaban APC.
