Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarnin a gaggauta sake duba farashin kuɗin aikin Hajjin shekarar 2026.
Shugaban ya umurci Hukumar Hajji ta Kasa (NAHCON) da ta fito da sabon farashi cikin kwanaki biyu.
Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ne ya miƙa umarnin na shugaban ƙasa a lokacin wani taro da ya gudanar tare da shugabannin da kuma membobin hukumar NAHCON a Fadar Shugaban Kasa, da ke Abuja, a ranar Litinin.
Ya bukaci a haɗa kai tsakanin jami’an hukumar na ƙasa da na jihohi, ciki har da gwamnonin jihohi, wajen tsarawa da kuma amincewa da sabon tsarin farashin aikin Hajjin, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Haka kuma, ya jaddada buƙatar ɗaukar matakin gaggawa daga dukkan bangarorin da abin ya shafa domin tabbatar da biyan kuɗaɗe da aika su ga Babban Bankin Najeriya (CBN) cikin lokaci, don gudanar da aikin Hajji ba tare da wata matsala ba.
Da yake amsa tambayoyin ‘yan jarida bayan kammala taron da Mataimakin Shugaban Kasa, Mataimakin Shugaban Ma’aikata na fadar gwamnatin tarayya, Sanata Ibrahim Hadejia, ya bayyana cewa an gudanar da taron ne da nufin kammala shirye-shiryen aikin Hajjin 2026, musamman wajen tantance farashin aikin.
Ya bayyana cewa manufar ita ce rage farashin kuɗin aikin Hajji domin maniyyata su samu sauƙin biya, la’akari da yanayin matsin tattalin arziki da ake fama da shi sakamakon sauye-sauyen da gwamnati mai ci ta fito da su.

