
Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya ce babu wani mutum da zai iya canza abin da Allah Ya ƙaddara.
Shugaban ƙasar ya faɗi haka ne a yayin jana’izar Lydia Yilwatda, mahaifiyar shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda.
An gudanar da jana’izar ne a ranar Asabar, inda Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, tare da wasu gwamnoni, ‘yan majalisa, jami’an gwamnati da sauran manyan baki suka halarta.
A cikin jawabinsa, Shugaba Tinubu ya ce yawan manyan bakin da suka halarci bikin ya nuna yadda mutane ke girmama mahaifiyar shugaban jam’iyyar.
“Wannan taron ya kamata ya tunatar da mu muhimmancin ɗabi’u irinsu haɗin kai, gamsuwa, farin ciki, da jagoranci nagari ga ƙasarmu.”
“Ga limamai kuwa, ina godiya bisa sakon natsuwa da kuka isar, da kuma ƙoƙarinku wajen ƙarfafa zaman lafiya, kwanciyar hankali, da abota. Kiɗa da ƙiyayya ba zaɓi ba ne a gare mu. Abin da dole ne mu ci gaba da wa’azi a kai shi ne soyayya — soyayya ga juna.”
