
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sallami Janar Christopher Musa, Babban Hafsan Tsaro na ƙasa, tare da wasu daga cikin manyan hafsoshin tsaro.
Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da sadarwa, Sunday Dare, ya fitar a ranar Juma’a.
A cewar sanarwar, an maye gurbin Musa da Janar Olufemi Oluyede, wanda kafin nadinsa, shi ne Babban Hafsan Sojan Ƙasa.
An nada Manjo Janar W. Shaibu a matsayin sabon Babban Hafsan Sojan Ƙasa, yayin da Air Vice Marshal S.K. Aneke ya zama sabon Babban Hafsan Sojan Sama, sai Rear Admiral I. Abbas wanda aka nada a matsayin sabon Babban Hafsan Sojan Ruwa.
Sai dai Babban Hafsan Leken sirri, Manjo Janar E.A.P. Undiendeye, ya ci gaba da riƙe muƙaminsa.
