
Wani ɗan jarida a jihar Kano, Ibrahim Dan’uwa Rano, ya shiga hannun ‘yan sanda a ofishin shiyya na rundunar ‘yan sanda da ke Kano, bayan da babban daraktan Gwamnan Kano Abdullahi Rogo, ya shigar da ƙara yana zargin ɗan jaridar da ɓata masa suna.
Yanzu haka hukumomin EFCC da ICPC na gudanar da bincike kan Mr. Rogo kan zargin almundahanar naira biliyan 6.5.
‘Yan sanda sun yi awon gaba da ɗan jaridar ne a lokacin da yake aiki a ofishinsa a Kano ba tare da nuna masa takardar kamu ba, inda suka kai shi ofishin rundunar ‘yan sanda na shiyya domin yi masa tambayoyi.
Majiyoyi sun bayyana cewa ana yi wa Mr. Rano tambayoyi ne kan zargin ɓata suna da kuma gudanar da gidan talabijin na intanet ba tare da samun lasisi daga Hukumar Kula da kafafen yaɗa labarai ta ƙasa NBC ba.
Kodayake Mr. Rano ya shaida wa ‘yan sanda cewa ba ya buƙatar lasisin NBC domin buɗe tashar intanet ko gudanar da shirye-shiryen intanet, amma ‘yan sanda sun tsare shi, bisa umarnin babban daraktan.
