
Shugabancin Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya ASUU ya umarci dukkan rassanta a faɗin kasar da su fara yajin aikin gargaɗi na makonni biyu daga ranar Litinin.
Shugaban ƙungiyar ASUU na ƙasa, Farfesa Chris Piwuna, shi ne ya sanar da hakan a taron manema labarai da aka gudana a hedkwatar kungiyar da ke Jami’ar Abuja.
Piwuna ya ce an ɗauki wannan matakin na fara yajin aikin gargaɗi na gama-gari ne saboda gazawar gwamnati wajen aiwatar da abubuwan da kungiyar ke bukata.
