Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya ce a shirye ya bar wa matashi takara shugaban ƙasa, idan ya faɗi a zaben fidda gwani na jam’iyyar ADC a gabanin babban zaben 2027.
Da yake jawabi a wata hira da BBC Hausa ta yi da shi a ranar Laraba, Atiku, wanda tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa ne na jam’iyyar PDP a zaben 2023, ya kuma ce an yi sauri wajen tabbatar ko zai sake tsayawa takara ko kuma akasin haka, amma ya jaddada cewa haɗa kan ƴan adawa a ƙarƙashin ADC shi ne babban burinsa yanzu.
“Wannan tafiya yanzu aka fara. Abin da muka fi bai wa muhimmanci shi ne kafa jam’iyyar da kuma samun goyon baya mai ƙarfi.
“Idan na tsaya takara, matashi ya kayar da ni, zan amince da hakan.
“Jam’iyyar da muka shiga yanzu tana bai wa matasa da mata muhimmanci.” a cewa Atiku.
